Majalisar Dattawa ta koka kan lalacewar manyan hanyoyin gwamnatin tarayya

Majalisar Dattawa ta koka kan lalacewar manyan hanyoyin gwamnatin tarayya

Majalisar dattawa a Najeriya ta koka matuka kan lalacewar manyan titunan gwamnatin tarayya a fadin kasar. Majalisar ta bayyana damuwar hakan ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba yayin zaman da ta gudanar cikin birnin Abuja.

Shugaban majalisar dattawan, Sanata Ahmed Lawan, ya bukaci gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gaggauta shimfida dokar ta-baci akan lalacewar manyan hanyoyin kasar.

Sanata Lawan ya bayyana damuwar hakan da cewa ya kamata gwamnatin tarayya ta yi gyaran manyan hanyoyin kasar kyakkyawan tanadi ta hanyar ware kasafi na makudan kudi, lamarin da ya ce akwai bukatar a kowace shekara a ware kimanin Naira biliyan 200 domin inganta hanyoyin kasa.

Wannan babatu ya biyo bayan korafin da Sanata Gershom Bassey na jihar Cross River ya gabatar, inda ya koka akan mummunan yanayin da manyan titunan gwamnatin tarayya ke ciki a kasar.

KARANTA KUMA: Liberia ta fi kowace kasa a duniya karrama baki - Bincike

Sanata Bassey ya kuma sanarwa da majalisar dattawan cewa hukumar PPPRA mai kula da daidaita farashin man fetur ta gaza aika koda kaso biyar da na kudaden hukumar kula da hanyoyin tarayya (FERMA), kamar yadda aka tsara a dokar gyara titunan kasar.

A yayin zartar da hukunci, majalisar dattawa ta umurci kwamitinta akan kula da albarkatun man fetur tare da hadin gwiwar hukumar FERMA, da su binciki zargin rashin aika kudin daga PPPRA don gyara hanyoyi a kasar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel