Liberia ta fi kowace kasa a duniya karrama baki - Bincike

Liberia ta fi kowace kasa a duniya karrama baki - Bincike

A wallafar rahoton jaridar BBC Hausa, wata gidauniyar jinkai da rajin karamci mai tushe a kasar Birtaniya, ta bayyana kasar Liberia ta yankin Yammacin Afirka, a matsayin kasar da ta fi kowace kasa a duniya taimako da karrama baki.

Wannan sabon rahoton na zuwa ne biyo bayan wani bincike da gidauniyar jinkan ta Birtaniya ta gudanar.

Babu shakka taimakon baki na daya daga cikin abubuwa guda uku da gidauniyar ke amfani da su wajen fayyace matakin karamcin kasashen duniya ko kuma sabanin haka.

Haka kuma gidauniyar ta yi duba kan yawan adadin kudaden da al'umma ke sadaukar wa domin shirye-shiryen jinkai da kuma gudunmuwar taimakon wasunsu ta hanyar sa-kai.

A tsawon shekaru goma da gidauniyar ta shafe wajen gudanar da binciken, ta gano cewa kasar Liberia ce ta fi kowace kasa a duniya karamci bayan sauraron ra'ayin mutane kimanin miliyan 1.3 a duniya.

KARANTA KUMA: Ronaldo ya fi kowane dan kwallo samun kudi a duk sakon da ya wallafa a Instagram

Binciken ya kuma haskaka cewa kasar Kenya ta fi kowace kasa kirki a nahiyyar Afirka, inda ta kasance kan sahu na 11 a duniya baki daya.

Sauran kasashen nahiyyar Afirka da suka shiga cikin sahun gaba a kasashen duniya mafi kirki sun hadar da; Liberia wadda ta kasance a mataki na 17, Sierra Leone a na 20 yayin da Najeriya ta tsinci kanta a mataki na 22.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel