Ronaldo ya fi kowane dan kwallo samun kudi a duk sakon da ya wallafa a Instagram

Ronaldo ya fi kowane dan kwallo samun kudi a duk sakon da ya wallafa a Instagram

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Juventus kuma dan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo, shi ne dan wasan da ya fi kowane dan kwallon kafa samun kudi ta hanyar daya daga cikin dandalan sada zumunta na zaman wato Instgaram.

A rahoton da jaridar The Nation ta ruwaito, Ronaldo ya sha gaba wasu fitattun 'yan kwallo wadanda ya yi zarra gami da fintinkau wajen samun makudan kudade ta hanyar sakonnin da ya wallafa a zauren na Instagram.

Ronaldo mai shekaru 34 wanda ya kasance tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, ya sha gaban wasu zaratan 'yan kwallon kamar su Zlatan Ibrahimovic, Neymar, Ronaldinho da kuma babban abokin adawarsa a fagen kwallo, Lionel Messi.

A shekarar da ta gabata kadai, Ronaldo ya samu kimanin Fan Miliyan 38 ta hanyar sakonnin da ya wallafa a dandalin instagram, wanda ya ninku sau biyu kan kudin da Messi ya samu.

Wani sabon bincike na baya bayan nan ya tabbatar da cewa, cikin jerin mutane da suka fi kowa shahara a duniya, Ronaldo ya sha gaban dukkaninsu wajen samun kudi ta hanyar duk wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Za mu ci gaba da neman taimakon kasashen duniya - Buhari

Binciken Buzz Bingo ya gano cewa, gamayyar wallafe-wallafen da Ronaldo ya yi a shekarar da ta gabata kan shafinsa na Instagram, dan wasan ya samu Fan miliyan 38.2 wato dai Fan 780,000 a kan kowace wallafa daya.

Ana iya tuna cewa, a makon da muke ciki ne Ronaldo ya ci kwallo ta 700 a ranar Litinin yayin wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a karawar da Portugal ta yi da kasar Ukraine.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel