Direbobin bankaura: Hukumar FRSC ta kama yan Achaba 728 a jahar Kaduna

Direbobin bankaura: Hukumar FRSC ta kama yan Achaba 728 a jahar Kaduna

Hukumar kare haddura ta kasa reshen jahar Kaduna ta kama yan Achaba guda 728 a jahar Kaduna dake yawo a garin Kaduna ba tare da mallakan lasisin tuki ba, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar FRSC tana cewa a cikin makonni 2 kadai, adadin yan Achaba da masu tuka keke napep 521 sun mallaki lasisin tukin nasu, kamar yadda shugaban hukumar na Kaduna, Haffiz Mohammed ya bayyana.

KU KARANTA: Gwamna Aminu Tambuwal zai kafa jami’ar likitanci ta Mata zalla a Sakkwato

Mohammed ya bayyana cewa hukumar ta fara samar da lasisin ne sakamakon wani muhimmin aikin rajistan ababen hawa da suka kaddamar a fadin kasar Najeriya gaba daya.

Kwamandan yace hadakan hukumomin FRSC, Civil Defence, Yansanda da kuma jami’an hukumar tattara haraji ta jahar Kaduna ne suka kaddamar da wannan aiki tun daga ranar 2 ga watan Oktoba zuwa 14 ga wata.

“Tun farkon fara wannan aiki mun kama babura da keke napep guda 728 a cikin garin Kaduna, zamu fadada wannan aiki zuwa manyan garuruwan jahar Kaduna, kamar su Kafanchan da Zaria nan gaba kadan, zuwa yanzu matuka babura da keke napep 631 sun yi rajista.

“Tunda muka fara wannan aiki bamu samu wata matsala ba sakamakon mun yi ta wayar da kawunan jama’a ta hanyar amfani da kafafen watsa labaru. Dole ne ababen hawa dake bin hanyoyinmu su kasance masu rajista ko don tsaro, haka zalika domin tabbatar da duk wanda ke tuka abin hawa yana da lasisi.” Inji shi.

Majiyarmu ta ruwaito a ranar farko da hukumomin suka fara gudanar da wannan aiki sun kama babura 100 masara lasisi a cikin garin Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel