Sabon salo: 'Yan sanda sun bukaci wata budurwa da ta nuna rasit din siyan karenta

Sabon salo: 'Yan sanda sun bukaci wata budurwa da ta nuna rasit din siyan karenta

- Wata budurwa da ta nuna tsananin fushinta ta wallafa yadda 'yan sanda suka tambayeta rasit din siyaen karenta

- Ta ce 'yan sandan sun bukaci takardun motarta inda ta bayyanasu ba gtare da wata matsala ba

- Amma sai suka koma tambayar shaidar siyen karenta da ke cikin motar

Wata budurwa a Najeriya ta nuna fushinta sakamakon tsareta da ‘yan sanda suka yi da cewa sai ta nuna takardar shaidar siyan karenta.

Kamar yadda budurwar ta sanar, ‘yan sandan sun nemi rasit din siyan karenta daga wajenta ne sakamakon rashin samun hanyar da zasu tozarta ta. Budurwar ta ce, sun bukaci takardun motarta kuma ta bayyanasu ba tare da wata mastala ba. Amma kwatsam sai suka tambayeta rasit din siyan karenta da ke cikin motar.

KU KARANTA: FG ta bayyana matatun man fetur 6 da zasu fara aiki a Najeriya

“Kai, ‘yan sandan nan basu da hankali. Yakamata ‘yan sanda su tsareka saboda kana dauke da kare a motarka? A wanne littafi ne aka ce musu akwai lasisin karnuka?” kamar yadda budurwa ta wallafa.

‘Wani dan sanda ya tsare ni a titi tare da tambayata rasit din siyan karena. A cewarsa, sato Karen nayi in dai banda takardar shaidar siyansa. A take na tambayeshi, a wanne littafi ne aka ce ku tambayi rasit din siyaen kare?” in ji budurwar.

Bai ga wata matsala tattare da takardun motata ba don haka yake son samun laifin da zai lakaba min, in ji budurwar kamara yadda ta wallafa a shafinta na tuwita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel