Gwamna Aminu Tambuwal zai kafa jami’ar likitanci ta Mata zalla a Sakkwato

Gwamna Aminu Tambuwal zai kafa jami’ar likitanci ta Mata zalla a Sakkwato

A kokarinta na tabbatar da kafuwar jami’ar likitanci ta mata zalla, gwamnatin jahar Sakkwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta sanar da aniyarta na samar da filin da za’a gina wannan jami’ar a matsayin nata gudunmuwar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gidauniyar SuItan ce za ta gina wannan jami’a a jahar Sakkwato, wanda ta sanya ma suna Jami’ar Nana Asmau, watau diyar mujaddadi Shehu Usman Danfodio.

KU KARANTA: Abu namu: Har Sanatoci sun kammala karatu na biyu ga kasafin kudin shekarar 2020

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan ya umarci ma’aikatar sifiyo da filaye da ta samar da filin da ya fi dacewa da gina wannan katafaren jami’a, a yayin da ya karbi bakuncin wakilan gidauniyar Sultan a ofishinsa dake fadar gwamnatin jahar.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal yace yana daga cikin manufofin gwamnatinsa ta cigaba da raya ayyukan tsofaffin shuwagabannin masarautar Sakkwato, tare da baiwa shuwagabannin yanzu kwarin gwiwar samar da ire iren wannan ayyukan cigaba.

Gwamnan ya kara da cewa tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, masarautar Sakkwato na da tsararren tsarin tafiyar da mulki, wanda wasu kasashe da dama suke koyi dashi.

A nasa jawabi, Sarkin Argungu, kuma shugaban sashin buga littafai na gidauniyar Sultan, Alhaji Samaila Muhammadu Mera ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin jahar Sakkwato bisa gudunmuwar data bayar wajen buga littafan hukumar guda 92.

Alhaji Mera ya yi addu’ar Allah Ya saka ma Gwamna Tambuwal da alherinsa, sa’annan ya kara da cewa littafan da aka bugasu guda 1,380,000 tuni gidauniyar ta rabasu ga manyan makarantun gaba da sakandari, Islamiyyu da kuma makarantun boko a kasashen Amurka da Abu Dhabi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel