Sule: Nakasassu za su rika karatu a manyan makarantu kyauta a Jihar Nasarawa

Sule: Nakasassu za su rika karatu a manyan makarantu kyauta a Jihar Nasarawa

Gwamnan jiahr Nasarawa, Abdullahi Sule ya kaddamar da shirin bada ilmi kyauta a fadin jihar ga duk wani nakasasshen da yake karatu a makarantu na gaba da sakandaren gwamnatin jihar.

Kamar yadda mu ka samu labari, gwamnan ya bada wannan sanarwa a Ranar Talata, 16 ga Watan Oktoba a Garin Akwanga a lokacin da Tawagarsa ta ziyarci kwalejin ilmin jihar da ke Garin.

Gwamnan ta bakin jami’an sa na yada labarai sun sanar da shugaban kwalejin da ke Akwanga watau Dr. Rebecca Isaac Umaru cewa gwamnati za ta rika daukar nauyin nakasassun kwalejin.

Duk wata dawainiyar gajiyayyen da ke karatu a wannan makaranta ta koma kan gwamnatin Abdullahi Sule don haka jami’an su ka nemi a ba su takardun kudin makarantar marasa karfin.

KU KARANTA: Daga zuwa Makaranta an nemi ‘Ya ‘ya matan wani mutumi a Taraba

Yanzu makarantar za ta karbi duk abin da wani nakasasshe ya kashe mata domin a maida masa kudinsa. Rebecca Isaac Umaru ta yabawa wannan tare da alkawarin ba gwamnati goyon baya.

Shugabar wannan kwaleji, Dr. Isaac Umaru ta mika kokon barar ta ga gwamnan inda ta nemi a ba su damar daukar manyan ma’aikata na din-din-din 11 wanda za su rika koyar da nakasassun.

Har ila yau, shugabar kwalejin ta yi alkawarin ba masu nakasa a makarantar kayan karatu da wurin kwana da duk sauran abubuwan da su ke bukata domin ganin sun yi karatu cikin sauki.

Hamza Mammam Awe wanda shi ne ke ba gwamna shawara kan harkar nakasassu a Nasarawa ya tabbatar da cewa gwamnatin Sule za ta maida hankali wajen inganta rayuwar marasa karfin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel