Abu namu: Har Sanatoci sun kammala karatu na biyu ga kasafin kudin shekarar 2020

Abu namu: Har Sanatoci sun kammala karatu na biyu ga kasafin kudin shekarar 2020

Kasafin kudin shekarar 2020 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ma majalisun dokokin Najeriya a makon data gabata har ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawan Najeriya, wai, tuwona maina kenan, inji masu iya magana.

Rahoton jaridar Daily Trust ta bayyana cewa bayan kammala karatu na biyu a kan kasafin kudin ne sai majalisar ta dage cigaba da zamanta zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba domin baiwa ma’aikatu da hukumomin gwamnati kare kasafin kudinsu a gaban kwamitocin majalisar.

KU KARANTA: Siyasa mugun wasa: An gano wani gwamnan APC dake kokarin ficewa daga cikinta

A jawabin daya gabatar na karshe a yayin zaman majalisar na ranar Talata, majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan yana bayyana cewa karancin kudi ne kadai zai kawo tsaiko ga wannan kasafin kudin.

Da yake magana ta bakin kaakakinsa, Ezrel Tabiowo, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa idan har ba a dauki wani kwakkwaran mataki ba, zai yi wuya a iya aiwatar da kasafin kudin kamar yadda aka tsara.

“Muna fuskantar kalubalen kudi, kuma da alamu idan ba wai mun dauki wani kwakkwaran mataki bane, matsalar karancin kudi zai cigaba da haifar da babbar matsala ga aiwatar da kasafin kudin.

“Don haka zamu cigaba da ganawa da hukumomin tattara harajin gwamnati, tare da auna ayyukansu a duk bayan watanni uku ta hannun kwamitocinmu, musamman kwamitin majalisar dattawa a kan harkokin kudi.

“Akwai kalubale babba duba da cewa kashi 30 kacal aka ware ma manyan ayyuka, amma duk da haka akwai cigaba idan aka yi duba ga kasafin kudin shekarar 2014, inda kashi 15 kacal aka ware ma manyan ayyuka, sai dai hakan ba wai yana nufin ba zamu iya yin abinda ya fi haka bane.” Inji shi.

Daga karshe Sanata Lawan ya yi kira da a duba yiwuwar rage ma’aikatu da hukumomin gwamnati da suka kai guda 600, amma ba tare da ragewa ko korar ma’aikata ba, domin a samu daman rage kaso mafi tsoka na kasafin kudi, watau kasafin dake kula da albashi da alawus alawus din ma’aikata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel