El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2020 ga Majalisar jihar Kaduna

El-Rufai ya gabatar da kasafin kudin 2020 ga Majalisar jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a jiya Talata 15 ga watan Oktoba ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 na biliyan N257 a gaban Majalisar dokokin jihar Kaduna.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakiyarsa, Dr Hadiza Balarabe ya ce, gwamnatinsa na da kudurin kashe naira biliyan 109.7 a kan ayyuka da ilimin jihar.

KU KARANTA:Gwamna Bello ya ware biliyoyin kudi domin yin aikin tituna a jihar Neja

Ya ce a karkashin kasafin kudin na 2020, shekara 12 na bayar da ilimin firamare da sakandare a jihar zai zama kyauta ga ko wane yaro.

Gwamnan ya kara da cewa, gwamnati za tayi amfani da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa iyaye su sa yaransu a makaranta, musamman a lokutan da ake tsakiyar karatu a makarantun.

A na shi jawabin, Kakakin majalisar dokokin, Aminu Abdullahi Shagali ya yabawa gwamnatin jihar Kaduna kasancewarta jihar farko da ta soma biyan sabon mafi karancin albashi a kasar nan.

Ya kuma bada tabbacin cewa majalisar za tayi adalci game da kasafin kudin sannan kuma za ta maido da shi cikin lokaci.

A wani labarin mai kama da wannan za ku ji cewa, Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello ya aminta da biyan biliyan N6 domin yin ayyukan tituna a jiharsa.

Wannan kwangilar za ta kasance ne tsakanin Bankin duniya, wata hukumar kasar Faransa, RAMP da kuma gwamnatin jihar Nejan, inda za ayi aiki a kan titunan da tsawonsu ya kai kilomita 230.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel