Siyasa mugun wasa: An gano wani gwamnan APC dake kokarin ficewa daga cikinta

Siyasa mugun wasa: An gano wani gwamnan APC dake kokarin ficewa daga cikinta

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomhole ya bayyana cewa gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki ya kammala shirye shiryen ficewa daga jam’iyyar tasu ta APC, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Oshiomhole ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Simon Ebegbulem, inda yace gwamnan na kokarin raba kan yayan jam’iyyar ne kafin ya tsallake daga cikinta.

KU KARANTA: Rikicin cikin gida: Ta tabbata Buhari ba zai iya rike gidansa ba balle Najeriya – PDP

“Muna da sahihin labarin cewa gwamnan yana shirin fasa jam’iyyar APC, sa’annan daya cimma wannan manufa tasa sai ya fice daga cikin jam’iyyar zuwa wata jam’iyya, a dalilin haka ne ya fara yin gaban kasa a dukkanin sha’anin mulki ba tare da duba da tanadin doka ba, kuma jama’an Edo ba zasu lamunta ba.

“Ina kira ga gwamnan ya daina bata min suna, ya mayar da hankalinsa ga tafiyar da sha’anin mulki wanda shine dalilin da yasa aka zabeshi, babban damuwarmu a yanzu ita ce yadda gwamnan ke neman tilasta min bayyana masa zirga zirgana, wa ya san abinda yake shirya min? amma duk wani sharrin da yake shirya min ba zai yi nasara ba.” Inji shi.

Bugu da kari Oshiomhole ya tabbatar da cewa an kai masa hari a gidansa dake garin Binia ranar 12 ga watan Oktoba, inda yace yan daban Obaseki ne suka aikata masa wannan cin mutunci har gida.

“Kafin wannan hari, gwamnatin jahar Edo tana amfani da yan daba suna cin zarafin yayan jam’iyyar APC a kananan hukumomin jahar 18, saboda shuwagabannin APC basu tabbatar masa da takararsa karo na biyu ba, haka zalika yana ta sallamar ma’aikata daga aiki.” Inji shi.

Sai dai kwamishinan Yansandan jahar, Danmallam Muhammad ya bayyana cewa babu wata hujja dake tabbatar da cewa yan daba sun kai ma Oshiomhole hari a gidansa kamar yadda yake ikirari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel