Za a sake sa rana bayan taron ‘Yan kwadago da Majalisa bai yi yiwu ba

Za a sake sa rana bayan taron ‘Yan kwadago da Majalisa bai yi yiwu ba

Mun samu labari daga Jaridar The Nation cewa yunkurin da ‘yan majalisar wakilan tarayya su ka yi na yin zaman sulhu da kungiyar kwadagon Najeriya a cikin farkon makon nan bai kai ga ci ba.

Shugaban kwamitin kwadago da aikin yin a majalisar wakilai, Honarabul Ali Wudil Mohammed, ya shaidawa Manema labarai cewa majalisa ba ta iya yin zaman da ta shirya da kungiyoyin ba.

‘Dan majalisar ya ke cewa shugabannin kungiyar kwadago na kasar sun aikowa kwamitin da yake jagoranta wasika, su na sanar da su cewa ba za su iya halartar taron da aka gayyace su ba.

Ali Wudil Mohammed ya kuma bayyana cewa kungiyar TUC ta ‘yan kasuwar kasar, wanda aka so a zauna da su, sun yi gum ba tare da sun sanar da majalisa abin da ya hana su zuwa taron ba.

KU KARANTA: Ma'aikata za su tafi yajin aiki idan gwamnati ta saba alkawari

Honarabul Wudil yace zaman yarjejeniyar da ma’aikatan kasar su ke yi da gwamnatin tarayya a game da batun karin albashi ne ya hana Jagororin NLC amsa goron gayyatar da aka kai masu.

A takardar da NLC ta aikowa majalisa a Ranar 15 ga Watan Oktoba, 2019, ta bayyana cewa taron da aka sa a jiya ya cabe ta zaman kwamitin JPSNC da gwamnatin tarayya kan sabon tsarin albashi.

Wannan ya sa NLC ta nemi a ba ta wata rana domin ta hallara gaban ‘yan majalisar a nan gaba. An karanto wannan wasika a zauren kwamitin majalisar tarayyar a jiya Litinin 15 ga Oktoba.

‘Ya ‘yan kwamiti na majalisar kasar sun nuna cewa a shirye su ke su sa baki domin ganin an karkare batun karin albashi. Wudil ya tabbatar da za su yi aikin da shugaban majalisar ya sa su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel