Masari ya roki FG kudi domin tallafawa wadanda 'yan bindiga suka yi wa barna

Masari ya roki FG kudi domin tallafawa wadanda 'yan bindiga suka yi wa barna

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta samar da kudaden da za a tallafawa mutanen da rikicin 'yan bindiga ya ritsa da su a jihohin Sokoto, Zamfara da Katsina.

Ya yi wannan rokon ne a wurin taron jin ra'ayoyin al'umma na kwana daya da Ma'aikatar Sadarwa na Tarayya tayi kan tsaro a ranar Talata a Katsina.

Masari ya ce, "Ina son inyi kira ga gwamnatin tarayya ta ware wani tallafi na musamman domin taimakawa mutanen da rikicin 'yan bindiga ya shafa a jihohin Arewa ta Yamma guda uku.

DUBA WANNAN: Abin kunya ne a ce Mamman Daura yana zaune a Aso Rock - Afenifere

"Idan gwamnatin ta amince, za a yi amfani da wannan kudin na musamman wurin samar da muhalli da sauran kayayyakin inganta rayuwa ga wadanda rikicin na 'yan bindiga ya shafa a jihohin.

"Za a kuma yi amfani da wani kaso na kudin domin biyan jami'an tsaro na musamman domin samar da zaman lafiya mai dorewa a jihohin uku.

"Za a kuma iya amfani da shi domin rage radadi ga al'ummar da abin ya shafa da wadanda suka tuba da iyalansu.

"Gwamnatocin jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara na bukatar taimakon kudi domin taimakawa mutanen da rikicin ya ritsa da su su koma gidajensu amma lamarin ya wuya a yanzu."

A bangarensa, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta bullo da wasu shirye-shirye da za su taimakawa mata su fara sabuwar rayuwa duba da cewa wasu sun rasa mazajensu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel