Kotun daukaka kara ta warware hukuncin bawa APC kujerar majalisa a jihar Bauchi

Kotun daukaka kara ta warware hukuncin bawa APC kujerar majalisa a jihar Bauchi

Kotun daukaka kara reshen jihar Jos ta soke hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben majalisar dokokin jihar Bauchi ta yanke a baya.

Kotun sauraron korafin zabe ta soke nasarar lashe zaben Umar Sarki na jam'iyyar PRP a matsayin dan majalisar wakilai ma wakiltar mazabar Katagum tare da mika ga jam'iyyar APC.

Kotun sauraron kararrakin zaben da ke Bauchi, ta soke zaben Sarki a ranar 29 ga watan Augusta a dalilin cewa, yakamata hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa zaben bai kammalu ba saboda soke sakamakon zaben akwatuna 7 da ta yi.

DUBA WANNAN: Karin albashi: Zan biya ma'aikatan jiha ta fiye da N30,000 - Zababben gwamnan APC

Kamar yadda kotun sauraron kararrakin zaben ta sanar, yawan kuri'un da aka soke, sun fi yawan kuri'un da ke tsakanin Sarki,wanda ya yi nasarar lashe zaben da Ibrahim Baba na jam'iyyar APC, wanda ya sha kaye a zaben.

Bayan rashin gamsuwa da hukuncin, Sarki ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara reshen jihar Jos akan dalilai biyar.

A hukuncin da masu shari'ar suka yanke wanda Jastis Boloukuromo Moses Ugo ya jagoranta, kotun ta yanke hukuncin da ya ba wanda ya daukaka kara nasara a matsayin wanda ya lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel