Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

Tirkashi: An tsinto wasu iyali da suka kebe tsawon shekaru 9 suna jiran 'karshen duniya'

'Yan sanda a kasar Netherlands sun gano wani mahaifi da yaransa shida da suke buya a wani gida na karkashin kasa a wani gidan gona da suka kwashe shekaru suna jiran 'karshen duniya' a cewar mahukunta a ranar Talata.

Sun gano wani mutum da aka kyautata zaton mai gidan ne da yaransa masu shekaru tsakanin 18 zuwa 25 a kusa da kauyen Ruinerwold a arewacin lardin Drenthe kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kafafen watsa labarai na kasar sun ce an gano iyalin ne yayin da daya daga cikin yaran ya tafi wani mashaya a gigice ya sha kwalaben giya biyar sannan ya roki mai mashayan ya taimake shi don wai ya shafe shekaru 9 bai fito waje ba.

DUBA WANNAN: Jerin sunaye: Mutum 5 da suka taba lashe kyautar Nobel a Afirka

'Yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 58 a gidan saboda ya ki bayar da hadin kai yayin binciken amma bai mai gidan bane.

Shugaban 'yan sanda Roger de Groot ya yi jawabi yayin taron manema labarai inda ya ce, "Ban taba ganin irin wannan abin a rayuwa ta ba."

"Yan sanda sun gudanar da binciken ne bayan wani mutum da ya damu da yanayin da suke rayuwa ya tsegunta musu," inda muka gano manyan mutane a cewar de Groot.

"Suna rayuwa ne a kebe," inji shi, ya kara da cewa sun kwashe shekaru tara suna rayuwa tare da yara da yawa 'kuma ba su taba rajistan sunayensu a rajistan haihuwa ba' ko wani rajista na gwamnati.

Akwai tambayoyi da dama da ba gano amsoshinsu ba a halin yanzu amma 'yan sanda suna gudanar da bincike, a cewar de Groot.

Gidan talabijin na TRV Drenthe da ya fara ruwaito labarin ya ce iyalan sun 'dade suna rayuwa a gidan karkashin kasa na tsawon shekaru suna jiran karshen duniya'.

Gidan talabijin din ya kara da cewa wasu daga cikin wadanda aka ceto daga gidan ba su san akwai sauran mutane a duniya bayan su ba.

Makwabta suna ce ba su san akwai mutane da yawa a gidan ba kawai wani mutum daya suke gani yana harkokinsa.

'Yan sanda ba su bayar da karin bayani ba a halin yanzu a yayin da AFP ta tuntube su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel