Gwamnati ba zata iya gamsar da 'yan Najeriya ba a bangaren harkar kiwon lafiya

Gwamnati ba zata iya gamsar da 'yan Najeriya ba a bangaren harkar kiwon lafiya

- Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasa, ya ce gwamnatin tarayya ba zata iya gamsar da 'yan Najeriya a bangaren harkar kiwon lafiya ba saboda yawan da yawan jama'ar da ake da shi

- Mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wurin wani taron tattauna wa a kan harkar lafiya da gidan jaridar Premium Times ta shirya a Abuja

- Ya kara da cewa burin gwamnatin Najeriya shine inganta bangaren harkokin kiwon lafiya domin anfanuwar dukkan 'yan kasa

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatin tarayya ba zata iya gamsar da 'yan Najeriya a bangaren harkar kiwon lafiya ba saboda yawan jama'a.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a wurin wani taron tattauna wa a kan harkar lafiya da gidan jaridar Premium Times ta shirya a Abuja.

Mataimakin shugaban kasar, wanda ya samu wakilin babban likitansa, Nicolas Audiferren, ya ce bullo da tsarin inshorar lafiya na kasa babban cigaba ne a harkar kiwon lafiya.

DUBA WANNAN: Zaben gwamna: Buhari ya nemi majalisa ta amince ya bawa gwamnatin APC a Kogi biliyan N10.069

"A bayyane take cewa gwamnatocin tarayya da na jihohi ba zasu iya gamsar da 'yan Najeriya a bangaren harkar lafiya ba, wannan shine gaskiyar zance.

"mafita kawai ita ce tsarin inshorar lafiya, ita ce kadai hanyar da zata kawa cigaba cikin sauri a bangaren harkar kiwon lafiya a Najeriya," a cewarsa.

Ya ce burin gwamnatin Najeriya shine inganta bangaren harkokin kiwon lafiya domin anfanuwar dukkan 'yan kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel