Rikicin cikin gida: Ta tabbata Buhari ba zai iya rike gidansa ba balle Najeriya – PDP

Rikicin cikin gida: Ta tabbata Buhari ba zai iya rike gidansa ba balle Najeriya – PDP

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP ta bayyana cewa barkewar rikici a cikin gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari tsakanin matarsa da yan uwansa ta nuna cewa ba zai iya rike Najeriya ba.

Legit.ng ta ruwaito PDP ta kara da cewa wannan fada daya fito fili tsakanin uwargida Aisha Buhari da Fatima, diyar Alhaji Mamman Daura ya nuna gazawar shugaban kasa Buhari wajen iya tafiyar da sha’anin mulki.

KU KARANTA: Gwamnati na kokari wajen samar da tsaro, amma ba’a gani – Minista

Da wannan ne PDP ta yanke hukuncin cewa ta tabbata shugaba Buhari ya gaza wajen kulawa da gidansa, don haka ya gaza tafiyar da Najeriya tare da al’ummarta zuwa tudun mun tsira, a sanadiyyar haka yan Najeriya suke ganin gwamma jiya da yau.

“Wannan rikici manuniya ce game da irin sabata-juyata da kuma yi ma doka karen tsaye da ake yi a fadar shugaban kasa cikin gwamnatin Buhari, haka zalika rikicin ya bankado yadda aka mayar da fadar shugaban kasa a bin wasa, wanda a baya aka santa da kima, bugu da kari ga shi an cikata da wadanda basu da hurumi a cikinta.

“A yanzu idon yan Najeriya ya bude sun fahimci dalilin da yasa aka kasa ganin wani cigaba a kasar, wannan kuma shine dalilin daya rudu, cin hanci da rashawa, kwan gaba kwan baya, kiyayya, da kuma rashin kwarewa a sha’anin mulki ya dabaibaye gwamnatin Buhari.” Inji Kaakakin PDP, Kola Ologbondiyan.

Da wannan ne PDP ta nemi shugaba Buhari ya yi gaggawar neman gafarar yan Najeriya bisa wannan rikici daga gidansa daya zubar da martabar Najeriya da yan Najeriya a idon duniya, sa’annan ya sauka daga mulki ya mikata ga hannun kwararru tunda dai ta tabba ba zai iya wani katabus ba.

Daga karshe PDP ta yi kira ga majalisun dokokin Najeriya su binciki yadda Buhari yake raba gidaje da ofisoshi ga mutanen da basu da hurumi a fadar shugaban kasa, sa’annan sun nemi yan Najeriya su kwantar da hankulansu saboda irin wannan badakala ya zo karshe da zarar kotun koli ta kwace mulkin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel