Hukumar INEC ta bayyana abunda ke firgita ta game da zaben gwamnan Bayelsa

Hukumar INEC ta bayyana abunda ke firgita ta game da zaben gwamnan Bayelsa

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta yi gargadi akan ayyuka da furucin yan siyasa, cewa hakan na iya wargaza zaman lafiya a lokacin gudanar da zaben gwamna na ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Bayelsa.

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Yakubu Mahmood, wanda yayi magana a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba a lokacin da ya ziyarci ofishin majalisar saakunan gargajiya dake Yenagoa, yace ayyuka da furucin yan siyasa na iya rusa zaman lafiya a lokacin zabe, jefa kuriu’u da tattara sakamako.

Mahmood wanda ya samu rakiyan jami’an hukumar da hukummin tsaro karkashin jagorancin mataimakin Inspekta Janar na yan sadan Zone 5, Dibal Yakadi, ya kuma yi korafi aka amfani da yan daba wajen tarwatsa tsarin jefa kuri’u da tattara sakamako.

Da yake bayyana Bayelsa da Kogi a matsayin jihohi mafi wahala wajen gudanar da zabuka, Mahmood ya cigaba da cewa hukumar ta damu matuka da mummunan lamari da ke tashe na siyan kuri’u inda yace lallai bai kamata a bude kasuwar cinikin damokradiyya ba.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta kashe N450bn wajen biyan rarar tallafin mai cikin 2020 – Ministar Buhari

Yace hukumar za ta tura ma’aikatan wucin gadi guda 10,000 a yankuna daban daban na jihar Bayelsa domin shirin zaben, inda ya kara da cewa INEC ba za ta bari kowa ya kai masu farmaki ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel