Karo na farko cikin shekaru 55, hukumar sojin sama ta samu mata matuka jirgin yaki (Hotuna)

Karo na farko cikin shekaru 55, hukumar sojin sama ta samu mata matuka jirgin yaki (Hotuna)

Hukumar Sojin saman Najeriya NAF ta karrama Kafayat Sanni a matsayin matukiyar jirgin saman yaki na farko a tarihi da Tolulope Arotile a matsayin matukiyar jirgi mai saukar angulu ta farko a tarihin Najeriya.

Jami'an sojin saman sun kammala horonsu ne a kasar Amurka da Afrika ta kudu. Suna cikin hafsoshin hukumar 13 da aka karrama a taron da ya gudana ranar Talata.

A taron, babban hafsa sojin saman Najeriya, AM Sadique Abubakar ya ce wannan sabon tarihi ne a shekaru 55 na hukumar.

Karo na farko cikin shekaru 55, hukumar sojin sama ta samu mata matuka jirgin yaki (Hotuna)
Karo na farko cikin shekaru 55, hukumar sojin sama ta samu mata matuka jirgin yaki (Hotuna)
Asali: Facebook

Yace:"Ina farin cikin na musamman saboda cikin matuka jirgi 13 da za'a yaye, biyu daga cikinsu mata ne,"

"Ba wai mata ne kawai ba amma kwararrun matuka. Yayinda daya daga cikinsu ce matukiyar jirgin saman yaki ta farko a tarihin hukumar NAF a shekaru 55, dayar ce matukiyar jirgi mai saukar angulu ta farko a tarihi."

" Matukiyar jirgin saman yaki ta farkon ta samu horo ne a hukumar sojin saman Amurka bayan namijin kokarin da tayi a horon da akayi musu a makarantar koyon tukin jirgi ta 401 dake Kaduna."

"A yanzu muna da matuka 61 da suka fara koyon tukin jirgi, yayinda 50 suke horo na koli a makarantun gida da kasar waje."

Ya ce a tarihin hukumar, sun horar da matuka 67 daga shekarar 2015 zuwa yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel