Yan sanda sun tisa keyar malamin cibiyar horar da dalibai na Daura zuwa Katsina

Yan sanda sun tisa keyar malamin cibiyar horar da dalibai na Daura zuwa Katsina

Rahotanni sun kawo cewa an dauke mammalakin cibiyar horar da kangararru da ke Daura, wanda ke azabtar da yara, Mallam Bello Umar, daga Daura zuwa hedkwatar rundunar yan sandan jihar Katsina domin cigaba da bincike.

An gano malamin mai shekara 78 a hedkwatar masu binciken kakkwafi na CID a safiyar Talata, 15 ga watan Oktoba.

Majiyoyin yan sanda abun dogaro sun bayyana cewa an dauke malamin zuwa hedkwatar rundunar ne domin ba yan sanda dammar samun Karin bayanai akan cibiyar horar da daliban, musamman akan ayyukan ta.

Sai dai majiyoyin basu sanar da lokacin da za a mika malamin da sauran mutane biyu da aka kama kotu ba.

Daya daga cikin majiyoyin da ya nemi a boye sunansa yace: “Shakka babu, za mu kais hi kotu, amma hakan ya danganta da lokacin da muka kammala binciken mu.

“Binciken ne kuma zai bayar da dammar tuhume-tuhumen da za a yi akansa da sauran mutanen.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta kashe N450bn wajen biyan rarar tallafin mai cikin 2020 – Ministar Buhari

“Har yanzu muna neman malama makarantar horon, domin akwai zargin luwadi a kan wasun su, baya ga zargin mugun azabtawa da daliban ke zarfinsu akai.”

Kwamishinan yan sandan Katsina, Sanusi Buba, ya kuma bayyana cewa an kai fursunonin zuwa wani asibiti domin duba lafiyarsu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel