Gwamna Bello ya ware biliyoyin kudi domin yin aikin tituna a jihar Neja

Gwamna Bello ya ware biliyoyin kudi domin yin aikin tituna a jihar Neja

Gwamna Abubakar Bello na jihar Neja ya aminta da fitar da naira biliyan 6 domin sabunta wasu titunan jihar Neja da tsawonsu ya kai kilomita 230.

Za a gudanar da ayyukan titunan ne a karkashin shirin Rural Access and Mobility Project wato RAMP domin rage fatarar ayyukan gina kasa a jihar.

KU KARANTA:Aso rock: Ku binciki hakikanin abinda ke faruwa a Villa, PDP tayi kira ga Majalisar dokoki

Kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN ta ruwaito cewa RAMP na shiga lungu da sako na kauyukan wasu garuruwan Najeriya domin yi ma titunansu gyara da kuma kwaskwarima.

Wannan kwangilar dai Bankin duniya ne tare da French Development Agency za su dauki nauyinta, yayin da RAMP kuwa ke tare da gwamnatin jihar Neja a fannin ganin an kyautata sufuri a kauyukan jihar.

Shugaban RAMP, Hassan Baba ya kara da cewa, gwamnan ya sake bada wasu kudi naira biliyan 1.6 domin biyan bashin alawus da kuma wadansu kudaden ma’aikatan, inda ya ce a baya gwamnatin ta biya miliyan N206 daga cikin miliyan N400m na gudunmuwa ta musamman.

Haka kuma ya fadi cewa, RAMP ta samu nasarar kammala aikin tituna masu tsawon kilomita 176 daga shekarar 2013 zuwa yau a fadin jihar ta Neja.

Bugu da kari, daga cikin kididdigar da Baba ya bamu ya ce kimanin mutum 728, 891 ne ke amfana da wannan shirin inda tabbatar mana da cewa a sanadiyar shirin an samu raguwar mace-mace musamman na mata a lokacin haihuwa.

“RAMP ba tituna kadai take yi ba, akwai ayyukan gina makarantu, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya. Haka kuma akwai inganta ayyukan noma ta hanyar amfani da kayayyakin zamani.” Inji shi.

https://dailynigerian.com/bello-approves-n6bn-for-road-projects-in-niger/

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel