Kogi: Ya kamata IGP ya fadawa CP ya shiga taitayinsa – Inji PDP

Kogi: Ya kamata IGP ya fadawa CP ya shiga taitayinsa – Inji PDP

Jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Kogi ta aikawa Sufeta Janar na ‘Yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, sako cewa ya ja kunnen Kwamishinansa na ‘Yan sanda da ke jihar Kogi.

PDP ta nemi IGP ya gargadi Kwamishinan ‘yan sandan na Kogi da ya daina marawa ta’addancin jam’iyyar APC baya a jihar. Austin Usman Okai ya zargi APC da amfani da ‘yan bangar siyasa.

Austin Usman Okai wanda shi ne Mataimakin Darektan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP ya fitar da wannan jawabi a Garin Lokoja a Ranar 13 ga Watan Oktoba.

Mista Usman Okai ya zargi ‘ya ‘yan jam’iyyar APC mai mulki a jihar da rabawa ‘yan daba bindigogi kwanaki a karamar hukumar Dekina domin a ruguza allon ‘yan takarar jam’iyyar PDP.

KU KARANTA: Mummunar barakar APC ta ci Garin Buhari da wasu Jihohi

Darektan na PDP ya yi ikirarin cewa wadannan ‘yan bangar siyasan sun zo ne dauke da makamai a cikin wasu dogayen motoci kirar Sienna tare da sanin jami’an tsaro amma su ka kauda kansu.

Jam’iyyar adawar ta zargi Kantoman Dekina watau Hon. Aboh, da labewa da sunan yakin neman zabe wajen kai wa ‘ya ‘yansu hari. PDP tace Abah sanannen ‘dan ta’adda ne a yankin Dekina.

“Shirin kai mana hari yunkurin jefa tsoro ne da dar-dar a cikin zukatan masu zabe da Magoya bayan PDP a kallon idon gwamnatin jihar Kogi. Wannan zai kai ga sauran kananan hukumomi”

“APC ne su ka bada umarnin fatattakar ‘Ya ‘yan PDP domin sun dauki zabe tamkar yaki. Wannan zai sa jama’a su gaza iya fitowa su zabi APC.” Usman Okai ya nemi ‘yan sanda su tashi tsaye.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel