Boko Haram: An kashe sojojin Najeriya 840 a cikin skara 6 - Sanata Ndume

Boko Haram: An kashe sojojin Najeriya 840 a cikin skara 6 - Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume, shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan harkokin rundunar soji, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya 847 daga shekarar 2013 zuwa yanzu.

Ya ce an binne sojojin da suka mutu a makabartar binne dakarun soji da ke cikin garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Ndume adadin sojojin bai hada da wadanda aka kashe kuma aka binne su a wasu makabartun sojoji ba.

Dan majalisar ya shaida wa manema labarai hakan ne bayan dawowar kwamitin da yake jagoranta daga jihar Borno.

Ya ce, a yayin ziyarar da suka kai, sun fahimci cewa ba a bawa sojojin Najeriya isassun kayan aikin da zasu tunkari mayakan Boko Haram ba.

Kazalika, Ndume ya bayyana cewa adadin sojojin da ke jihar Borno ya yi kadan su gama da Boko Haram, tare da yin kira a kan gwamnati ta kara yawan rundunar sojojin.

Ya kara da cewa tuni kwamitinsa ya fara binciken zargin wasu kungiyoyin agaji na kasa da kasa da hannu a cikin yakin Boko Haram da gwamnatin Najeriya.

A cikin watan Satumba ne rundunar sojin Najeriya ta rufe ofishin wasu kungiyoyin agaji biyu; 'Mercy Corps' da 'Action Against Hunger', bisa zarginsu da taimakon mayakan kungiyar Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel