Buhari ya amince da amfani da jirage marasa matuka a iyakokin Najeriya

Buhari ya amince da amfani da jirage marasa matuka a iyakokin Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da amfani da jirage marasa matuka da jiragen yaki na musamman da fasahar sararin samaniya domin kiyaye iyakokin Najeriya kamar yadda aka ruwaito a ranar Talata.

The Nation ta ruwaito cewa wata majiya ta ce tsarin yana cikin shirin e-Customs ne da za ayi amfani dashi domin hana shige da ficen haramtattun kayayyaki da mutane ta iyakokin Najeriya.

Bayan sayo na'urorin da kuma amfani da e-Customs, ana sa ran samun ingantaccen tsaro a kan iyakar kasar wadda hakan zai kore bukatar gina katanga a iyakokin kasar.

Majiyar ta ce: "Shugaban kasa ya amince da e-Customs. E-Customs ya kunshi amfani da jirage marasa matuka da wasu jiragen sama da kuma amfani da fasahar sararin samaniya domin sanya idanu a kan iyakokin Najeriya domin hana shiga da ficen haramtattun kayayyaki da mutane. Da zarar anyi haka ina tabbatar maka cewa za mu tsaro a iyakokin mu kuma babu bukatar gina katanga."

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

Wannan na zuwa ne bayan kaddamar da atisayen hadin gwiwa na operation Ex Swift Response.

Ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro (ONSA) ce ke jagorantar atisayen da ya kunyi 'yan sandan Najeriya, Jami'an Kwastam, Immigration, Rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro domin magance matsalar tsaro a iyakokin kasar.

Shugaban hukumar kula da shiga da ficen mutane, Mohammed Babandede a wurin taron manema labarai a Abuja kan Operation Ex Swift Response ya ce Shugaba Buhari ya amince da aiwatar da dokokin ECOWAS na shige da fice.

A cewar dokar idan mutum ba shi da takardun tafiya, Jami'an Immigration ba za su bari ya fice daga Najeriya ba kuma ba za a bari wadanda ba su da takardun su shigo kasar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel