Fani-Kayode ya bukaci Buhari da ya yi kokarin kare Aisha daga masu far mata

Fani-Kayode ya bukaci Buhari da ya yi kokarin kare Aisha daga masu far mata

Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode ya shawarci Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya shiga cikin rikicin da ke tsakanin matarsa, Aisha da ‘yar kawunsa Mamman Daura, wato Fatima.

Fani-Kayode, wanda ya kasance jigo a babban jam’iyyar adawar kasar ta Peoples Democratic Party (PDP), ya kuma fada ma Buhari cewar yayi kokarin kare matarsa daga masu kai mata hari.

A cewar Fani-Kayode shi ba zai taba yarda wani ya zagi ko ya farma matarsa ba.

Ku tuna cewa Fatima ta zargi Aisha Buhari da cin mutuncin iyalanta, cewa Aisha ta far masu a cikin Aso Rock.

Da take magana a kan wani faifan bidiyon da Aisha ke masifa a cikinsa saboda an rufe mata kofar shiga dakinta, Fatima ta ce ta yi mamakin irin yadda matar shugaba kasa ta rufe ido take ta masifa.

KU KARANTA KUMA: Abin kunya ne a ce Mamman Daura yana zaune a Aso Rock - Afenifere

Faifan bidiyo ya kewaya a dandalin sada zumunta a daidai lokacin da ake rade-radin cewa shugaba Buhari zai angonce da Sadiya Umaru Farouq, sabuwar ministar harkokin tallafi da walwalar 'yan kasa.

A wata hira da ta yi da sashen Hausa na BBC, Fatima ta ce ta nadi faifan bidiyon ne domin ya zamar mata hujja a kan cewa Aisha ta yi musu 'tatas' a cikin fadar shugaban kasa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel