Operation Python Dance: An bai wa daruruwan sojoji horo a jihar Imo domin su kula da yankin Igbo

Operation Python Dance: An bai wa daruruwan sojoji horo a jihar Imo domin su kula da yankin Igbo

Daruruwan sojoji tare da wasu jami’an tsaro sun samu horo a Kudu maso gabashin Najeriya domin su fara aiki tare da tawagar Operation Python Dance a karo na hudu.

Majiyar Vanguard ta tattaro mana bayanan cewa, a jiya Litinin 14 ga watan Oktoba ne Kwamandan rundunar Garrison ta 82 ya jagoranci horon wanda a rundunar atilare ta 34 dake Obinze a birnin Owerri.

KU KARANTA:Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta ja labule da kungiyar kwadago

Birgediya Janar, Sylvester Oloyede ya ce an horar da sojojin ne domin sake karfafa tsaro a yankin Kudu maso gabas na Igbo. Ya bayyana abubuwan da yankin ke fama da su kamar garkuwa da mutane, ta’addanci da dai sauransu.

Oloyede ya kara da cewa, duka a cikin tsarin bayar da horon akwai duba lafiyar jama’ar yankin, tsaftace muhallinsu da kuma gyaran wasu daga cikin titunansu da suka lalace sakamakon ambaliya.

A cewar Oloyede: “Ina yi maku maraba da zuwa runduna ta 82 domin samun horo na musamman. Ina godiya ga Allah da ya bamu ikon gudanar da wannan abu a yau.

“Kamar yadda dai kuka sani, kasar nan na fama da matsalolin tsaro iri daban-daban wadanda suka hada da; satar mutane, ta’addanci, fashi da makami da sauransu. Wannan horon na zuwa ne a karkashin umarnin Hafsun sojin kasa na Najeriya Laftanal janar T.Y Buratai.

“Babbar manufar wannan shirin shin ne rage aukuwar miyagun laifuka a yankin Kudu maso gabashin Najeriya. Kuma haka zai sake karfafa alaka tsakanin hukumomin tsaro daban-daban.” Inji Kwamandan.

https://www.vanguardngr.com/2019/10/hundreds-of-army-trained-in-imo-ready-for-python-dance-in-igboland/amp/?__twitter_impression=true

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel