A ba Sojin da aka kora daga aiki Miliyan 10 – Kotun ECOWAS ga Najeriya

A ba Sojin da aka kora daga aiki Miliyan 10 – Kotun ECOWAS ga Najeriya

Mun ji cewa kotun shari’a na ECOWAS ya yanke hukunci da cewa gwamnatin Najeriya ta biya kudi har Naira miliyan 10 ga wani Soja da aka taba sallama daga aiki a kasar mai suna Pte Eli.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN ta bayyana rahoton wannan shari’a a wani jawabi da ta fitar a Ranar 14 ga Watan Okotoba, 2019. An kuma nemi a biya tsohon Sojan bashin da yake bi.

A hukuncin da Alkali ya yi, ya nemi a biya Sojan da aka sallama daga aiki a 2012 bayan ya rasa bindigarsa. Wannan laifi ne ya sa manyan sojin kasar su ka kama wannan Jami’i su ka garkame.

A wancan lokaci Sojoji sun yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a irin kotunsu. Wannan ya sa tsohon jami’in tsaro ya daukaka kara zuwa babban kotun kungiyar ECOWAS ta Nahiyar.

Bayan sauraron wannan kara mai lamba ta ECW/CCJ/APP/44/16, Alkali ya nemi a biya sa kudi domin ya rage zafi. Bugu da kari kotu ta nemi hukuma ta maida masa duk wasu tarin hakkokinsa.

KU KARANTA: Ma'aikata su na wani zaman kus-kus da Gwamnati kan karin albashi

Alkalin ya umarci gwamnati ta fito da albashi da alawus din wannan Soji tun daga watan Maris na 2015 zuwa lokacin da aka fito da shi daga daurin da kuliya ta ce an yi sa ba bisa kan hakki ba.

Sai dai Mai shari’a Gberi-Be Ouattara ya yi watsi da wasu karar da tsohon Sojan Najeriyan ya shigar. Sauran wadanda su ka saurari karar su ne Dupe Atoki da mai shari’a Januaria Costa.

Mai karar ya fadawa kotu cewa an sace masa bindigarsa ne a lokacin da ya ke bakin aiki a Garin Riyom da ke jihar Filato. Wannan ya sa Alkalai su ka soki matakin daure shi na wani lokaci.

Gberi-Be Ouattara da yake yanke hukuncin karshe ya tabbatar da cewa babu inda aka sabawa shari’a wajen damke Pte Ali har zuwa tsaresa. Amma yace ba a bi doka kafin a garkame shi ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel