FG ta bayyana matatun man fetur 6 da zasu fara aiki a Najeriya

FG ta bayyana matatun man fetur 6 da zasu fara aiki a Najeriya

- Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, kananan matatun man fetur 6 ne zasu fara aiki gadan-gadan

- Idan za a tuna, gwamnatin da ta gabata ta bada akalla lasisi 35 ga kananan matatun man fetur din amma aka kalmashe tare da ajesu

- Yunkurin fara aikin kananan matatun za a iya dangantas a ne da cire harajin da gwamnatin tarayya ta yi musu

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, kananan matatun man fetur 6 da ta bawa lasisi zasu fara aiki a kasar nan don cika alkwarin shugaban kasa, Muhammadu Buhari na habaka yankin Niger Delta.

Babban mai bada shawar na mussamman ga shugaban kasar akan harkokin yankin Niger Delta, Edobor Iyamu ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

Iyamu ya ce, Buhari a shirye yake don ganin ya tabbatar da cewa mutanen Niger Delta sun amfana da damammakin da suke dasu a yankin mai albarkar man fetur.

KU KARANTA: Wani kamfanin sadarwa yayi kira ga babban bankin Najeriya akan biyan shi tarar $285m

“Gwamnatin tarayya ta cika lakawarinta awajaen ganin cewa ba lasisi kadai aka bawa matatun man fetur ba kadai, har da goyon bayansu wajen ganin sun fara aiki. Gwamnatin tarayya ta tabbatar da samuwar wajen da zai ja hankalin masu saka hannayaen jari,” in ji shi.

Kamar yadda ya ce, “Kada mu manta, a gwamnatin da ta gabata, an bada lasisin kananan matatu 35 inda ka kalmashesu aka aje. Sunyi hakan ne saboda suna morar romon tallafin man fetur. Sannan kuma tsarin gwamnatin na cire haraji ya jawo hankalin masu zuba hannayen jari yankin,”

“A yau ina farincikin sanar da cewa, kananan matatun man fetur muke dasu kuma da kain anej na gani ba wai a kafafen yada labarai na ji ba.” Iyamu ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel