Kasa kaurin shinkafa: Kotu ta bada umarin rufe asusun bankuna 45 mallakar wasu kamfanoni 3

Kasa kaurin shinkafa: Kotu ta bada umarin rufe asusun bankuna 45 mallakar wasu kamfanoni 3

Wata babbar kotun tarayya dake Abuja, ta bayar da umarnin rufe asusun bankuna guda 45 mallakar wasu kamfanoni uku da ake zargi da hannu wajen fasa kwaurin shinkafa a kasar.

Wadannan kamfanoni da abun ya shafa sun hada da; Sun Sam A1 International Limited, Sam Sun International Limited da kuma Sunchrist O. Trans Nigeria Limited.

An bada umarni ruke asusun su da ke cikin wasu bankunan zamani.

Alkalin kotun, Justis Mohammed Ahmed ya umarci hedikwatar kowane banki daga cikin bankunan 10 da kada su kuskura su bari a yi wata hada-hada a wadannan asusu, daga yanzu har zuwa nan da kwanaki 45.

Kotu ta ce asusun guda 45 za su ci gaba da kasancewa a rufe, har zuwa lokacin da Babban Bankin Najeriya (CBN) zai kammala binciken sa.

Lauyan CBN Nosike Nicholas ya nemi kotun ta bada umarnin kulle asusun guda 45 tsawon kwanaki 90. Sai dai kuma Mai shari’a ya amince da kwanaki 45 ne kawai.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da mataimakin shugaban majalisar dattawa

Alkali ya ce ya bayar da kwanaki 45 ne amma idan har kwanakin suka cika ba tare da CBN ya kammala binciken sa ba, to za a iya kara wani wa’adin ci gaba da kulle asusun idan CBN ya nemi karin wa’adin.

Lauya Nosike ya ce CBN na ci gaba da bincike a kan asusun ajiyar kamfanonin uku. Sannan kuma irin hada-hadar da su ke yi za ta ita gurgunta shirin noman shinkafa a kasar nan da kuma tattalin arzikin kasar shi kan sa.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel