Gwamnati na kokari wajen samar da tsaro, amma ba’a gani – Minista

Gwamnati na kokari wajen samar da tsaro, amma ba’a gani – Minista

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa yan jaridu basa yayata cikakken rahoton namijin kokarin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari take yi game da yaki da matsalolin tsaro a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ministan watsa labaru da al’adun gargajiya, Lai Mohammed ne ya bayyana haka yayin taron babban zaure na masu ruwa da tsaki daya gudana a garin Katsinan jahar Katsina a ranar Talata.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: Ministocin Buhari guda 3 sun dira jahar Katsina don gane ma idanunsu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito ministan ta ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a yayin bude taron, wanda gwamnatin tarayya ta shirya da hadin gwiwar gwamnatocin jahohin Katsina, Zamfara, Sakkwato da Kaduna.

A jawabinsa, Lai yace taron zai bada dama ga masu ruwa da tsaki su tofa albarkacinsu bakunansu wajen bada shawarwari game da hanyoyin da suka fi dacewa domin kawar da matsalolin tsaro da suka yi ma Arewacin Najeriya dabaibaye, musamman ma matsalar yan bindiga.

Wannan taro dai shi ne irinsa na 16 da gwamnatin tarayya ta shirya da nufin lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaro a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, kuma ya samu halartar ministocin tsaro, watsa labaru da na cikin gida.

Haka zalika gwamnonin jahohin Katsina, Sakkwato, Zamfara da Kaduna sun halarta, kamar yadda manyan hafsoshin rundunonin Sojan kasa, sama, ruwa, da kuma Yansanda duk suka samu halarta.

A wani labarin kuma, ministoci guda uku a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun kai wata muhimmiyar ziyara jahar Katsina domin halartar babban taron zaure inda zasu tattauna da jama’an Katsinawa game da matsalar tsaro da ake fuskanta a jahar.

Ministocin nan sun hada da ministan tsaro Bashir Magashi, ministan watsa labaru Lai Mohammed da kuma ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, kuma sun kai wannan ziyarar yini daya ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel