Zaben gwamna: FG za ta bawa gwamnatin jihar Kogi biliyan N10

Zaben gwamna: FG za ta bawa gwamnatin jihar Kogi biliyan N10

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika wa majalisar dattijai wasikar neman amincewar ta domin ya mayar wa gwamnatin jihar Kogi biliyan N10.069 domin biyan bashin da ake binsu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugaba Buhari ya aika wasikar ne zuwa majalisar a yayin da ya rage saura kwanaki 31 a yi zaben gwamna a jihar Kogi.

Za a gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi a ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019.

A cikin wasikar da shugaban majalisar dattijai, Ahmed Ibrahim Lawan, ya karanta yayin zaman majalisar dattijai na ranar Talata, ya ce za a mayar wa da gwamnatin jihar Kogi kudaden ne domin ta biya basussukan da ke kan ta.

Gwamnan jihar Kogi, Yahata Bello, yana takarar gwamnan a karkashin inuwar jam'iyyar APC a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel