An kuma: 'Yan bindiga sun sace yara 3 tare da kashe wasu 2 a Abuja

An kuma: 'Yan bindiga sun sace yara 3 tare da kashe wasu 2 a Abuja

- A yau ranar tallata ne aka tashi da alhini a kauyen Yebu da ke karamar hukumar Kwali da ke babban birnin tarayyar Najeriya

- 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun kutsa kauyen inda suka kashe mutane 2 tare da awon gaba da yara 3

- Shugaban karamar hukumar ya nuna tashin hankalinsa tare da kiar aga jami'an tsaro da su binciko masu hannu a aika-aikar

‘Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace yara uku tare da kasha wasu biyu a kauyen Yebu da ke Kwali a birnin tarayyar Najeriya.

Ayuba Danlami, mazaunin yankin, yace al’amarin ya faru ne wajen karfe 1:33 na daren Talata. 'yan bindiga masu yawan gaske sun shiga kauyen da miyagun makamansu.

Ya ce, ‘yan bindigar sun kutsa daya daga cikin gidajen kauyen tare da kashe mutane biyu inda suka yi awon gaba da yara uku duk daga gida daya.

KU KARANTA: Yadda aka koma amfani da kujerar roba don daukan marasa lafiya a UNTH

Kamar yadda yace, wadanda aka kashen sun yi yunkurin bi ta hanyar baya ne don sanar da mutane kauyen abinda ke faruwa. Ganin haka ne daya daga cikin ‘yan bindigar ya bude musu wuta har suka mutu a take.

“A takaice dai, ba mu iya barci ba a daren jiya saboda karar harbe-harben bindiga da ya cika kauyen” in ji shi.

Shugaban karamar hukumar yankin, danladi Chiya, ya tabbatarwa da manema labarai sace yara 3 da kasha mutane 2 a tattaunawar waya da ya yi da wakilin jaridar Daily Trust.

Ya ce, daya daga cikin wadanda aka kashen, magoyin bayan jam’iyyar APC ne don haka ma ya kasa barci bayan ya samu labarin rasuwarsa.

“A halin yanzu hawaye nake, daya daga cikin magoya bayan APC ya rasa ransa sanadiyyar kutsen cda ‘yan bindiga suka yi a kauyen. In akira ga jami’an tsaro da su zurfafa bincike don gano masu hannu a kisan da aka yi akauyen Yebu, “ in ji shi.

Mai Magana da yawun hukumar yan sandan birnin tarayyara bai masa way aba yayin da ake kiransa don jin ta bakinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel