Gwamnatin tarayya za ta kashe N450bn wajen biyan rarar tallafin mai cikin 2020 – Ministar Buhari

Gwamnatin tarayya za ta kashe N450bn wajen biyan rarar tallafin mai cikin 2020 – Ministar Buhari

Rahotanni da muke samu ya nuna cewa Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirinta na kashe wasu damin kudade har naira biliyan 450 wajen biyan kudaden tattafin man fetur a cikin shekarar 2020.

Ministar kudi, Zainab Ahmed ce ta sanar haka, duk kuwa da kokarin da gwamnatin ke yi na cewa za ta gyara dukkan matatun man kasar , domin a daina shigo da tataccen man fetur daga kasashen ketare.

Idan za a tuna, tsohon ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya bayyana cewa NNPC zai daina shigo da tataccen man fetur daga waje zuwa cikin kasar nan a cikin 2019. Amma dai duk da cewa ba a sake nada shi minista ba, har yau ba a daina shigo da man ba, kuma babu ranar dainawa, domin 2019 ta kusa kaiwa karshe.

Ministar kudin ta yi wannan karin haske kan damin kudaden da za a kashe a 2020 har naira bilyan 450 wajen biyan kudaden tattafin mai, wato ‘subsidy’, a wurin wani taron karin haske kan kasafin kudin 2020 da aka gudanar a Abuja.

Zainab ta yi wannan bayani ne a lokacin da Shugaban Kungiyar Masu Masana’antu na Kasa (MAN) Mansur Ahmed, ya tambaye ta shin ko an cire biyan kudin tallafin mai, ko kuwa har yanzu ana biya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da mataimakin shugaban majalisar dattawa

Kudaden dai a karkashin gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ana yi musu inkiya da kiran su kudaden cike gurbi, domin a karkashin wannan gwamnati ta sa, NNPC ce da kan ta kadai ke shigo da mai daga waje.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel