Abin kunya ne a ce Mamman Daura yana zaune a Aso Rock - Afenifere

Abin kunya ne a ce Mamman Daura yana zaune a Aso Rock - Afenifere

Kungiyar Yarabawa ta Afenifere ta yi tsokaci kan abinda 'yar Mamman Daura ta fadi na cewa sun kwashe a kalla shekaru uku suna zaune a fadar shugaban kasa inda ta ce hakan abin kunya ne.

Afenifere ta cigaba da cewa abin takaici ne mutumin da zababbe bane ya yi kane-kane a fadar shugaban kasar yana juya akalan gwamnati kamar yadda First Lady, Aisha Buhari ta fadi a baya cewa wasu tsiraru ne suka juya akalar mulkin kasar.

Mai magana da yawun Afenifere, Mista Yinka Odumakin ya yi wannan jawabin ne yayin wata hira da Punch tayi da shi a ranar Talata.

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

Odumakin ya ce, "Abin takaici ne Najeriya ta kai matsayin da mutumin da ba zabensa aka yi ba kuma ba a nada shi wani mukammi ba a karkashin kudin tsarin mulkin kasar mu ya samu irin wannan karfin.

"Babban abin kunya ce yadda wasu mutane da ke zaune a fadar shugaban kasa ba bisa ka'ida ba suna hira da manema labarai. Hakan yana nuna yadda lamura suka baci a kasar. Hakan ya nuna yadda aka ci mutuncin gidan shugaban kasar mu."

Odumakin ya ce yanzu da wannan sabon bayanin ya fito fili, ya rage da 'yan Najeriya su dauki matakin da ya dace su zaba idan suna son wasu daban da basu zaba ba su rika mulkansu ko kuma suyi fatali da 'cabal' din da ke juya kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel