Wani kamfanin sadarwa yayi kira ga babban bankin Najeriya akan biyan shi tarar $285m

Wani kamfanin sadarwa yayi kira ga babban bankin Najeriya akan biyan shi tarar $285m

- Kamfanin sadarwar Interstella communication Ltd, ya yi kira ga babban bankin Najeriya da ya yi biyayya ga hukuncin kotun koli

- Tun a watan Disamba na shekarar 2017 aka yankewa babban bankin hukuncin tarar $285m da zai biya kamfanin sadarwan wanda har a yau shiru kake ji

- Kamfanin ya ce rashin biyayyar ga dokar kotun zata iya jawo zubewar kimar kasar nan a idon duniya

Wani kamfanin sadarwa mai suna, Interstella communications Ltd, ya yi kira ga babban bankin Najeriya da su yi biyayya ga kotun koli ta hanyar biyansu tarar $285 miliyan da aka yanke hukunci a sakamakon zarginsu da ka da karantsaye ga kwangila.

A ranar 15 ga watan Disamban 2017 ne kotun koli ta yankewa babban bankin najeriyar hukuncin biyan tarar dala miliyan dari biyu da tamanin da biyar ga kamfanin sadarwa na Insterstella da Obi Thompson.

KU KARANTA: Gwamna Ganduje yayi magana akan yaran jihar Kano da aka samo a Anambra

A yayin zantawa da manema labarai a ranar Litinin, Tony Nnadi, shugaban lauyoyin masu kara na shari’ar ya ce, an yi duk kokarin cda ya dace wajen ganin babban bankin Najeriya ya yi biyayya ga hukuncin amma ya ki.

“Wannan abun zai iya jawo cece-kuce a duniya game da nagartar masana’antun kasarmu da kuma yadda suke daukan hukuncin kotu,” Nnadi yace.

Ya ce, babban bankin Najeriya ya ki maida martini ga wasiku uku suka tura msishi.

“A sakamakon hakan ne, wadanda suke bin babban bankin Najeriyar bashi zasu yi amfani da wata hanyar don tirsasa gwamnatin tarayyar biyayya ga dokar kotun kolin,” in ji lauyan.

An yi shari’ar ne sakamakon zargin cewa an karya yarjejeniyar kwangila tsakanin kamfanin sadarwar da babban bankin Najeriya inda kamfanin sadarwar ya yi nasara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel