Toh fah: Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta-baci a hanyoyinta

Toh fah: Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta-baci a hanyoyinta

Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta sanya dokar ta-baci akan hanyoyin tarayya a fadin kasar. Yan majalisa a majalisar dattawan ne suka gabatar da wannan bukata a yau Talata, 15 ga watan Oktoba yayin zaman majalisar dokokin a Abuja.

Hakan ya biyo bayan wani jawabi da Sanata Gershom Bassey daga jihar Cross River ya gabatar, inda ya koka akan mummunan yanayin da hanyoyin tarayya ke ciki a kasar.

Sanata Bassey ya kuma sanarwa da majalisar dattawan cewa hukumar kula da daidaita farashin man fetur (PPPRA) ta gaza aika kaso biyar da ake chaji na famfon mai zuwa ga hukumar kula da hanoyin tarayya (FERMA) , kamar yadda aka tsara a dokar gyara hanyoyin tarayya.

Da take zartar da hukunci, majalisar dattawa ta umurci kwamitinta akan man fetur da FERMA da su binciki zargin rashin aika kudin daga PPPRA don gyara hanyoyi a kasar.

KU KARANTA KUMA: Makwabci ya harbe wani dalibi dan Najeriya har lahira kan kure sautin waka a Amurka

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, ya yi ganawar sirri tare da mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege.

Sun fara ganawar ne da misalin karfe 12:30 na rana a fadar Shugaban kasa da ke Abuja. Motar Omo-Agege ya isa harabar fadar Shugaban kasar da misalin 12:08 na rana.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel