Matsalar tsaro: Ministocin Buhari guda 3 sun dira jahar Katsina don gane ma idanunsu

Matsalar tsaro: Ministocin Buhari guda 3 sun dira jahar Katsina don gane ma idanunsu

Ministoci guda uku a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari sun kai wata muhimmiyar ziyara jahar Katsina domin halartar babban taron zaure inda zasu tattauna da jama’an Katsinawa game da matsalar tsaro da ake fuskanta a jahar.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito ministocin nan sun hada da ministan tsaro Bashir Magashi, ministan watsa labaru Lai Mohammed da kuma ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, kuma sun kai wannan ziyarar yini daya ne a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: Ka taimaka a dawo min da sarautata – Maja sirdi ga Sarkin Kano

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewa a kwanakin baya an samu yawaitan kai hare haren satar shanu, matsalar garkuwa da mutane, da kuma kisan babu gaira babu dalili a jahohin Zamfara, Sakkwato, Kaduna da kuma uwa uba Katsina.

Wata sanarwa daga ma’aikatar watsa labaru da al’adun gargajiya ta bayyana cewa an kirkiri wannan tattaunawa ne da nufin lalubo bakin zaren game da wannan babbar matsala dake ruruwa a yankin Arewa maso yammacin kasar.

“Wannan taro na musamman an shirya shi ne da nufin samar da wani yanayi da jama’a za su yi tsokaci dangane da tsare tsare da ayyukan gwamnatin, haka zalika taron zai baiwa jama’a damar yin gyaran fuska ga manufofi da kudurorin gwamnati.” Inji sanarwar.

Daga karshe ana sa ran gwamnonin Sakkwato, Zamfara da Kaduna za su halarci wannan muhimmin taro domin bayyana hanyoyin da suke ganin ya dace a bi don shawo kan matsalar.

A wani labari kuma, dalibai guda hudu da suka rage a hannun wasu gungun yan bindiga da suka yi awon gaba dasu daga jahar Kaduna sun tsira sakamakon artabu da aka sha tsakanin dakarun rundunar Sojan kasa da yan bindigan a cikin daji.

Yan bindigan sun yi awon gaba da dalibai 14 ne daga makarantar sakandari ta gwamnati dake garin Gwagwada cikin karamar hukumar Chikun na jahar Kaduna a ranar Alhamis, 10 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel