A jihar Zamfara, za'a kafa dokar hukuncin kisa kan masu wulakanta Al-Kur'ani

A jihar Zamfara, za'a kafa dokar hukuncin kisa kan masu wulakanta Al-Kur'ani

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta kafa dokar haddi kan duk wanda aka kama yana wulakanta AlKur'ani a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayinda yake karban rahoton kwamitin da ya nada na duba ayyukan ma'aikatar harkokin addini karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar, Mallam Ibrahim Wakkala Muhammad.

Matawalle ya ce ran shi ba baci kan yadda wasu ke wulakanta Al-Kur'ani mai girma a jihar.

Ya ce matakin da za'a dauka domin kawo karshen wannan abu shine kafa dokar kisa ga duk wanda aka kama da laifin.

Ya kara da cewa za'a sanyawa Alkalan kotunan Shari'a ido kan yadda suke yanke hukuncin kan kararraki irin wannan kuma duk alkalin da aka kama da kokarin yin ba daidai zai fuskanci fushin hukumar.

Matawalle ya yi kira ga Malaman addinin Musulunci a jihar su rika wayar da kan mutane kan muhimmancin zaman lafiya, hadin kan da soyayyan juna saboda samun rayuwa mai dadi.

KU KARANTA: Ana saura wata daya zabe, Buhari zai ba gwamnatin jihar Kogi N10bn

A wani labarin daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara, yace ana gudanar da bincike sarakuna biyar da hakimai 33, bisa zarginsu da hannu a fashi da makami.

A wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, gwamnan yace yan sanda hudu da sojoji 10 ma na karkashin bincike akan wannan dalili guda.

Yace duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel