Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da mataimakin shugaban majalisar dattawa

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya shiga labule da mataimakin shugaban majalisar dattawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, 15 ga watan Oktoba, ya yi ganawar sirri tare da mataimakin Shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege.

Sun fara ganawar ne da misalin karfe 12:30 na rana a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Motar Omo-Agege ya isa harabar fadar Shugaban kasar da misalin 12:08 na rana.

Har yanzu Mataimakin Shugaban majalisar dattawan na a ofishin Shugaban kasa a daidai lokacin kawo wannan rahoton.

KU KARANTA KUMA: Zaben gwamnan Kogi: APC ta yi babban kamu na mambobin PDP har su 500

A wani labari na daban, mun ji cewa shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 36 su ka yi da Sakataren gwamnatin tarayya, a Garin Abuja, ya kare carko-carko ba tare da an iya cin ma wata matsaya ba.

Daga wani muhimmin zama da aka yi jiya 13 ga Watan Oktoban 2019, Jaridar ta samu labarin cewa har yanzu ba a kawo karhen rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC mai mulkin kasar ba. Shugabannin jihohi na jam’iyyar APC sun zauna da SGF Boss Mustapha ne bayan cikar wa’adin da su ka ba Adams Oshiomhole domin ya duba korafe-korafe da koke-koken da su ka gabatar.

A zaman da aka yin a Ranar Lahadi, an shafe tsawon sa’o’i ba tare da an kai ga ci ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel