Babu yunwa a Najeriya, inji ministan Noma, Sabo Nanono

Babu yunwa a Najeriya, inji ministan Noma, Sabo Nanono

Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono a ranar Litinin ya ce Najeriya tana samar da iasasun abinci da za ta iya ciyar da al'ummar ta har ma ta aike da saura zuwa kasashen da ke makwabtaka da ita.

The Punch ta ruwaito cewa Nanono ya ce koken da 'yan Najeriya ke yi na yunwa a kasar abin dariya ne inda ya ce babu yunwa a Najeriya.

Yayin jawabin da ministan ya yi a wurin taron manema labarai don bikin ranar Abinci na Duniya ta 2019 a Abuja, ya ce, "Ina tunanin muna noma wadataccen abinci da zai ciyar da mu. Ina ganin babu yunwa a Najeriya. Idan naji mutane suna maganar yunwa a wannan gwamnatin, na kanyi dariya ne kawai."

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

A cewar Nanono, abinci yana da araha sosai a Najeriya idan aka kwatanta da sauran kasashe.

Ya ce, "A kasar nan, babu tsadar siyan abinci da mutane za su ci."

Ya ce gwamnatin tarayya ta rufe iyakokin kasar ne domin saka dokokin da kasashen da ke makwabtaka da Najeriya keyi inda suka mayar da Najeriya bolar zubar da shinkafa da ta lalace da sauran kayayyaki.

Nanono ya ce, "Wannan shine ainihin dalilin da yasa aka rufe iyakokin kasar kuma ina ganin Najeriya tayi kokarin fahimtar da kasashen amma ba su yarda ba.

"Muddin har kasashen ba za su mutunta Najeriya suyi biyaya ga dokokin shige da fice ba kan shigo da abinci, iyakokin Najeriya za su cigaba da kasance a rufe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel