Yanzu-yanzu: Ana saura wata daya zabe, Buhari zai ba gwamnatin jihar Kogi N10bn

Yanzu-yanzu: Ana saura wata daya zabe, Buhari zai ba gwamnatin jihar Kogi N10bn

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci sa hannun majalisar dattawa kan baiwa gwamnatin jihar Kogi N10.069 billion na alkawari da yayi.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar shugaba Buhari a zauren majalisa.

Za'a gudanar da zaben jihar Kogi ranar 16 ga watan Nuwamba, 2019.

A wani labarin mai kama da haka, Kungiyar kamfen din gwamnan jihar Kogi na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), tace tana da karfin gwiwar cewa Gwamna Yahaya Bello zai yi nasara a zaben jihar mai zuwa.

Kingsley Fanwo wanda ya kasance Shugaban labarai na kungiyar kamfen din ne ya bayyana hakan a Lokoja, jaridar The Nation ta ruwaito.

A cewar Fanwo, APC ta samu Karin goyon baya daga mutane jihar da manyan masu ruwa da tsaki wanda zai taimaka wa gwamnan wajen samun tazarce.

Ya bigi kirjin cewa Gwamna Bello ne kadai zai iya kayar da kansa a zaben mai zuwa, inda ya kara da cewa dawowar yan takarar da suka kara da gwamnan a lokacin zaben fidda gwamni ya kara bunkasa damar APC na yin nasara sosai.

Fanwo yayi ba a ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), cewa jam’iyyar ta rasa shugabanninta da dubban magoya bayanta a hannun APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel