Yadda aka koma amfani da kujerar roba don daukan marasa lafiya a UNTH

Yadda aka koma amfani da kujerar roba don daukan marasa lafiya a UNTH

- Wani hoto da wani ma'abocin shafin tuwita yasa, ya jawo cece-kuce a kafar sada zumuntan

- Hoton kujerar roba ce da aka koma amfani da ita don daukan marasa lafiyan da aka kawo magashiyyan rai a hannun Allah

- Wasu na ganin hakan a matsayin ci baya inda wasu ke kallon hakan a matsayin fasaha da kirkirarriyar dabara

Hoton kujerar roba da ake zargi ana amfani da ita don daukar marasa lafiyan da aka kawo asibiti magashiyyan ya bazu a shafukan sada zumunta.

Kujerar robace da aka hada ta da karafunan tsohuwar kujerar daukar marasa lafiya.

Hoton kuwa ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta domin wasu na ganin hakan a matsayin wata hanyar tabarbarewa ko gazawar ma’aikatar lafiya ta Najeriya.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na dade a kasar waje - Aisha Buhari

Wani ma’abocin shafin tuwita ne dai ya saka hoton inda ‘yan Najeriya suka dinga fadin tsokacinsu tare da albarkacin bakinsu kan cigaban.

Mawallafin ya rubuta: “Asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya da ke jihar Enugu ya samu cigaba. Ni kadaoi ne na lura da hakan?”

Babu jimawa mutane suka fara tsokaci da cece-kuce akan hoton.

“Wannan tozarta kai ne, a misalin mutum mai kiba yahau kujerwar nan, me aka tsammanin zai faru?”

Wasu kuma a wani bangaren ganin fasahar duk wanda ya shirya wannan dabara suke.

“Wannan kirkirarriyar fasaha ta yi. Duk da dai cewa, za a iya maye gurbin kujerar da abunda yafi roba kwari”.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel