Rigimar Jam’iyyar APC ta yi karfi a Jihohin Shugaban kasa da Oshiomhole

Rigimar Jam’iyyar APC ta yi karfi a Jihohin Shugaban kasa da Oshiomhole

Daily Trust tace taron da shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 36 su ka yi da Sakataren gwamnatin tarayya, a Garin Abuja, ya kare carko-carko ba tare da an iya cin ma wata matsaya ba.

Daga wani muhimmin zama da aka yi jiya 13 ga Watan Oktoban 2019, Jaridar ta samu labarin cewa har yanzu ba a kawo karhen rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar APC mai mulkin kasar ba.

Shugabannin jihohi na jam’iyyar APC sun zauna da SGF Boss Mustapha ne bayan cikar wa’adin da su ka ba Adams Oshiomhole domin ya duba korafe-korafe da koke-koken da su ka gabatar.

A zaman da aka yin a Ranar Lahadi, an shafe tsawon sa’o’i ba tare da an kai ga ci ba. Bayan kammala taron, shugabannin jam’iyyar sun ki yi wa ‘yan jarida jawabi kamar yadda su ka saba.

Bayan taron da aka yi shekaran jiya, an ga shugabannin jam’iyyar su na yi wa Boss Mustapha rakiya. Haka zalika fuskokin jagororin jam’iyyar cike yake da annashuwa a daidai wannan lokaci.

KU KARANTA: Ana so kotu ta haramtawa APC da Gwamnanta takara a zaben Kogi

Manema labarai sun tuntubi jagororin bayan zaman na su amma ba su amsa kiran wayarsu ba. Wannan ya nuna cewa har yanzu barakar ta ke cikin gidan na APC na nan ba ta kwanta ba.

A takardar da shugabannin jihohin su ka sa hannu kwanaki, sun nemi a yabawa kokarin da su ka yi a zabe, sannan kuma sun bukaci a yi maza a maye gurbin tsohon Sakatare Mai Mala Buni.

Ali Bukar Bolari da Ben Nwoye wadanda ke shugabantar jam’iyyar APC a jihohin Borno da Enugu su ne ke jagorantar tafiyar shugabannin jam’iyyar inda su ke kukan an jefar da su bayan cin zabe.

Rrigimar ta fi karfi a jihohin Katsina da Edo. Daga cikin koken shugabannin Jihohin shi ne kin kiran taron NEC da ya kamata a rika yi sau uku a shekara. Rabon da ayi wannan zama tun bara.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel