Zaben gwamnan Kogi: APC ta yi babban kamu na mambobin PDP har su 500

Zaben gwamnan Kogi: APC ta yi babban kamu na mambobin PDP har su 500

Rahotanni sun kawo cewa akalla mambobin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) guda 500 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Lokoja da ke jihar Kogi.

Masu sauya shekar, wadanda suka ce sun yanke shawarar ne domin nuna biyayyarsu ga Gwamna Yahaya Bello, sun samu tarba daga Mista Muhammed Danasabe Muhammed, jagoran karamar hukumar, a Anguan Power, Lokoja.

Muhammed, wanda ya wakilci gwamnan, yace masu sauya shekar sun yanke shawara mai kyau ta hanyar dawowa ga jam'iyyar cigaba.

Ya basu tabbacin cewa jam'iyyar zata tabbatar da adalci da daidaito ga dukkan mambobinta a koda yaushe, ba tare da la'akari da lokacin da suka shigo jam'iyyyar ba.

Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Bello ba zata ba mambobin kunya ba ta hanyar aiwatar da shirye-shirye da manufofin da za su kawo cigaba ga jama'ar jihar.

Muhammed ya bukaci mambobin jam'iyyar da su cigaba da kimtsa kansu da kuma aiwatar da abubuwan da za su kare martabar jam'iyyar.

Ya kalubalanci sabbin mambobin jam'iyyar da su tabbatar da ganin an samu karin mutane da za su sauya sheka zuwa jam'iyyar, inda ya kara da cewa gwamnatin ba zata hana adawa ba domin siyasa tafi dadi idan akwai abokan hamayya da yawa.

KU KARANTA KUMA: Rufe iyakar kasar: An bukaci manoma da kada su kara farashin shinkafa

Jagoran masu sauya shekar, Alhassan Gimba, ya bayyana cewa sun koma APC ne biyo bayan tarin nasaraorin da Gwamna Bello ya samu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel