A gabana suka yiwa kanwata fyade sannan suka kashe mahaifina - Budurwa ta bayyana halin da suka shiga bayan 'yan bindiga sun kai musu hari har gida

A gabana suka yiwa kanwata fyade sannan suka kashe mahaifina - Budurwa ta bayyana halin da suka shiga bayan 'yan bindiga sun kai musu hari har gida

- Wata budurwa ta bayyana irin halin da ta shiga a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai musu hari kauyensu

- Budurwar ta bayyana yadda suka yiwa mahaifinta yankan rago bayan sun gama yiwa kanwarta fyade a kan idonta

- Ta ce har yanzu tana fama da tunanin wannan tashin hankali da ya faru da su a wannan ranar a ranta

A lokacin da 'yan bindiga suka kai hari garin Ariri, dake karamar hukumar Bassa cikin jihar Filato da misalin karfe 11:30 na dare. Kowa yayi tunanin cewa jami'an tsaro ne.

Bayan sunji harbe-harbe a cikin garin sai suka gane cewa 'yan bindiga ne suka kawo musu hari.

An bayyana cewa 'yan bindigar sunje gidan wani mutumi mai suna Samuel Agho, inda suka yi masa yankan rago bayan yayi kokarin kare 'yarshi daga fyaden da suke kokarin yi mata.

A wata hira da aka yi da daya daga cikin 'ya'yan mutumin mai suna Helen Agho, ta bayyana wannan hari da aka kai musu a watan Oktobar shekarar 2018 yadda ya canja musu rayuwa.

Ta ce: "A wannan ranar na dawo gida daga wajen aiki, na rufe kofar gidanmu kamar yadda iyayena suka bukaci na dinga yi a duk lokacin dana dawo gida ba da wuri ba.

"Da misalin karfe 11:30 na dare sai naji ana harba bindiga kusa da gidan mu da karfin tsiya, da farko nayi tunanin jami'an tsaron da suke zarya a yankin mu ne, amma kawai sai naji an sake harbawa wannan karon yafi wancan karfi, yayin da duka iyayena da 'yan uwana sun riga sun tashi a bacci. Sai muka fara addu'a tunda bamu san daga inda wannan karar bindiga ke zuwa ba.

"Ba a jima ba sai muka ji harbin bindigar na matsowa wajen gidan mu, mu kuwa mun dage da addu'a ba mu san cewa wannan ita ce addu'ar karshe da mahaifinmu zai yi ba. Kawai sai ganin mutane uku muka yi da wukake da sauran muggan makamai sun shigo gidan mu.

KU KARANTA: Kullum yayana na zuwa kan gadona idan ina bacci yayi ta wasa da azzakarinsa yana kokarin yin lalata dani

"Muna wajen a kwance sai daya daga cikin su yazo ya sanya mini bakin bindiga a kai na, haka sauran ma suka yiwa kannai na a yayin da daya daga cikinsu yake kokarin yiwa kanwata fyade, sai mahaifina yayi tsalle ya kama shi da kokawa."

A wannan lokacin sai ta ce mahaifiyarsu ce tace su fita daga gidan da gudu domin su tsira da kansu.

Ta cigaba da cewa: "Mahaifiyata da kakarmu suka fita daga gidan da gudu, inda ni kuma na tsaya na kasa gudu ina ihun neman taimako. A lokacin da wannan abu yake faruwa sai wani daga cikinsu ya kama kanwata yayi mata fyade, bayan ya gama abokinshi shima ya karba yayi mata.

"Bayan sun gama yiwa 'yar uwar tawa fyade sai suka yanka mahaifina suka fita abinsu.

"Na fito da gudu daga gidan na shiga wani gida dana ga kofar a bude na zauna a ciki har lokacin da gari ya waye. Har yanzu ban warke daga wannan tashin hankalin dana gani ba a wannan daren."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel