Kullum yayana na zuwa kan gadona idan ina bacci yayi ta wasa da azzakarinsa yana kokarin yin lalata dani

Kullum yayana na zuwa kan gadona idan ina bacci yayi ta wasa da azzakarinsa yana kokarin yin lalata dani

- Wata budurwa ta bayyana irin damuwar da take ciki bayan ta gano aika-aikar da dan uwanta wanda suke uwa daya uba daya yake kokarin yi da ita

- Budurwar ta gano cewa dan uwan nata yana kokarin yi mata fyade idan tana yin bacci

- Ta gano hakan ne bayan mahaifiyart ta sanar da ita cewa ta kama shi dumu-dumu yana wasa da azzakarinsa a kusa da ita a lokacin da take bacci

Wata budurwa wacce dan uwanta wanda suke uwa daya uba daya yake kokarin yi mata fyade ta koka inda take neman taimako akan wannan halayya ta dan uwan nata.

A cewar budurwar wacce ta roki a boye sunanta, ta bayyana cewa dan uwan nata yana kokarin yi mata fyade yayin da kullum yake zuwa kusa da ita yana wasa da azzakarinsa a yayin da ita kuma take yin bacci.

"Joro ka taimaka mini ka wallafa labari na, sannan kuma ka boye sunana. Dan uwana wanda muke uwa daya uba daya yana kokarin yi mini fyade, abin yana bani tsoro matuka. Lamarin ya fara jiya ne, mahaifiyar mu ta sanar dani cewa ta kama shi da rana lokacin da nake yin bacci ya zo kan gadona ya kwanta kusa dani ya fito da azzakarinsa yake yin wasa dashi a kusa dani.

KU KARANTA: Babbar magana: Kadan ya rage na kashe kaina bayan na kama saurayina yana zina da mahaifiyarsa - Budurwa

"A lokacin dana ji labarin nayi kuka matuka, sai naje na sami kawata nake sanar da ita abinda ke faruwa, sai take fada mini tunda har mahaifiyata ce ta fada mini to hakan na nufin ba shine karo na farko da ta kama shi ba.

"Sai na tambayi wata yarinya da muke kwanciya daki daya da ita sai take ce mini ai ta sha ganin shi yana zuwa yana yin wannan abin a kusa dani idan ina bacci.

"Hakan yasa nace ni kuma sai na kama shi watarana, aikuwa sai gashi ya shigo daki na, yana ganin na tashi sai ya gudu, sai ya sake dawowa, sai nayi amfani da wani sanda dana boye kusa dani na duke shi. Wallahi ban san ya zanyi ba, ku taimaka mini da shawarar hanyar da zan fitowa wannan lamarin," in ji budurwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel