Rufe iyakar kasar: An bukaci manoma da kada su kara farashin shinkafa

Rufe iyakar kasar: An bukaci manoma da kada su kara farashin shinkafa

Babban Bankin Najeriya (CBN) ta bukaci manoman shinkafa a fadin kasar da kada su kara farashin shinkafa sakamakon rufe iyakar kasar da aka yi.

A wani jawabi da ya gabatar a Abuja a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta, gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bukaci mambobin kungiyar manoman shinkafa na Najeriya (RIMAN) da sauran masu ruwa da tsaki a sana’ar da kada su boye shinkafa.

Gwamnatin Najeriya ta rufe iyakar kasar ta a watan Agusta, inda take bayanin cewa a hakan ne zata binciki shigo da kayayyaki ta haramtacciyar hanya.

Yayin da yake bayyana ra’ayinsa kan lamarin, Emefiele yace gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ne don bunkata tattalin arziki da kuma tabbatar da cewa kasar ta cimma isasshen abinci musamman a fannin noman shinkafa.

Yace akwai bukatar bunkasa noman shinkafa, inda ya sha alwashin cewa CBN zata goyi bayan masu noman shinkafa don kau da haramtacciyar hanyar shiga da kaya cikin kasar da kuma bunkasa sashin samar da isasshen abinci.

KU KARANTA KUMA: Ali ya ga Ali: Saraki ya hadu da Osinbajo da Tinubu a Lagas

Gwamnan CBN din yayi kira ga al’umm dasu goyi bayan rufe iyakar da gwamnatin tayi, inda yake cewa gwamnatin ta dauki matakin ne don amfanin su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel