'Yan takarar APC tarin 'yan ta'adda ne da 'yan kungiyar asiri, inji gwamnan PDP

'Yan takarar APC tarin 'yan ta'adda ne da 'yan kungiyar asiri, inji gwamnan PDP

Gabanin zaben ranar 16 ga watan Nuwamba a jihar Bayelsa, Gwamna Serike Dickson ya kwatanta 'yan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da 'yan kungiyar asiri, masu tayar da kayan baya da 'yan ta'adda.

A jawabin da gwamnan ya yi wurin taron kaddamar da yakin neman zaben gwamna na jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) a sakatariyar jam'iyyar a ranar Talata a ranar 14 ga watan Oktoba, ya ce jihar za ta fada cikin tashin hankali idan aka yi sake APC ta ci zabe a jihar.

Linda Ikeji Blog ta ruwaito Gwamna Dickson ya kara da cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba ta tsinana komi a jihar ba cikin shekaru 5 da suka gabata illa tashin hankali.

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

Ya ce, "Ku yi tunanin abinda zai faru idan abubuwa ba su tafi yadda muke so ba, duk cikin ku babu wanda zai iya maku daya a jihar Bayelsa. APC ta fitar da 'yan tayar da kayan baya, 'yan kungiyar asiri da masu laifi. Za su kafa gwamnatin 'yan daba ne da 'yan kungiyar asiri.

"Ba zai yi wu a mayar da dimokradiyya zuwa gwamnatin 'yan tayar da kayan baya da masu laifi ba.

"A yayin muke kaddamar da yakin neman zaben mu, za mu kaddamar da "Opertion wind APC a Bayelsa."

"Idan ko ba haka ba mutane za su rika tsoron ziyarar wannan jihar har 'yan garin za su rika tsoron zuwa jihohin.

"Idan ba mu dauki zaben da muhimmanci ba, a ranar 17 dukkan mu zamu bar jihar. Wannan zaben ba batun dan takara bane ko ni, muna yi ne saboda 'ya'yan mu da jikokinmu.

"A shekarar 2015 lokacin da nake takara, naga mutane da dama suna sauya sheka amma ina tabbatar muku zamu samu nasara. Amma hakan ba zai sa mu karaya ba domin mu za muyi nasara."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel