Kotu ta tsare wani tsoho mai shekaru 72 da ya yi wa 'yar cikinsa ciki

Kotu ta tsare wani tsoho mai shekaru 72 da ya yi wa 'yar cikinsa ciki

Kotun Majistare a Gombe a ranar Litinin ta bayar da umurnin tsare wani Ibrahim Yunusa dan shekaru 72 a gidan gyaran hali don zarginsa da yi wa 'yar cikinsa fyade har ta samu juna biyu.

Yununsa mazaunin Dadinkowa a karamar hukumar Yamaltu/Deba na jihar ya ce bai amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

Alkalin kotun, Daura Sikkam ya bayar da umurnin a bawa wanda ake zargin masauki a gidan gyran gali kuma ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Nuwamba domin a bawa 'yan sanda dama su kammala bincikensu.

DUBA WANNAN: Zaben Kogi: Hotunan Wada yana sharbar barci a wurin taro ya karade shafukan sada zumunta

A baya, magatakardan kotu, Dalaky Wanma yayin karanto rahoton 'yan sanda ya ce wanda ake zargin ya aikata laifin sau da yawa tsakanin watannin Disamban 2018 zuwa Janairun 2019.

Magatakardan kotun ya ce Yunusa ya hakikancewa 'yar sa mai shekaru 17 kuma ya yi mata ciki.

Wanma ya ce laifin ya sabawa sashi na 390 da 282 na dokar penal code.

Dan sanda mai bincike, Saja Bako Shekari shima ya shaidawa kotu cewa sun fara bincike a kan lamarin.

Ya roki kotu ta dage shari'ar domin a bawa 'yan sanda daman kammala bincike kuma su nemi shawara daga ma'aikatar shari'a na jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel