Rashin tashoshin ruwa ne yake dakatar da aikin kamfanin Dangote – LCCI

Rashin tashoshin ruwa ne yake dakatar da aikin kamfanin Dangote – LCCI

Rashin isassun tashoshin ruwa ne abin da ya kawo matsala wajen cigaban aikin ginin matatar da Aliko Dangote. Masu aiki da lura da matatar su ka bayyana wannan a Ranar 14 ga Oktoban 2019.

A Ranar 14 ga Oktoba ne ma’aikatan matatar su kace su na fama da kalubale wajen jigilar karafuna da sauran kayan aikinsu. Wannan matsala da ake fuskanta ya na kawowa kamfanin na su matsala.

Wani kwararren ma’aikacin hukumar LCCI ta Legas ya rubuta cewa wahalar da ake sha wajen dauko kaya masu nauyi ya na cikin kalubalen da ake fama da su a babbar matatar da ake ginawa a jihar.

Femi Ademola ya ce daukar karafuna masu nauyi a tashoshin ruwan ya kan zo da wahala don haka wannan ya zama ciwon kai ga Attajirin Afrika Aliko Dangote wanda ke katafaren aiki a Legas.

A dalilin wannan matsaloli ne aka rika daga lokacin da aka sa domin fara aiki a matatar danyen mai. Da farko Dangote ya sa rana cewa matatar za ta fara aiki a 2016 amma yanzu har an shiga 2019.

KU KARANTA: Abin da yake jawowa siyasar Atiku matsala - Song

Mista Ademola yace yanzu su na sa ran cewa za a karkare wannan namijin aiki a shekara mai zuwa ta 2020. Bayan haka matatar za ta iya soma aiki a 2021 zuwa cikin shekarar 2022 inji kwararren.

Demola Akinkunmi wanda yake aiki da Africa Port Services ya fadawa Manema labarai cewa kayan Dangote su na cika tashoshin ruwan kasar wanda hakan ke sa ana kara asarar makudan kudi.

Akwai hanyar ruwa da ake sa ran gwamnatin Legas za ta kammala domin rage cinkoso. Ana karbar $20, 000 a hannun masu jiragen ruwa duk rana ta Allah yayin da su ke kokarin sauke kayan aiki.

Da zarar Dangote y agama shigo da kaya, za a samu sarari a bakin tashohin ruwan kasar. Yanzu dai LCCI ta yi kira ga gwamnati ta gyara hanyoyi na tituna da kuma tashohin ruwan da ke jihar Legas.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel