Ka taimaka a dawo min da sarautata – Maja sirdi ga Sarkin Kano

Ka taimaka a dawo min da sarautata – Maja sirdi ga Sarkin Kano

Tun bayan bayyanar wasu rahotanni dake nuna cewa mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya tsige guda daga cikin hadimansa, watau Maja Sirdi, Alhaji Auwalu Idi, batun ya tayar da kura a fadar masarautar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa Sarkin ya tsige Maja Sirdi ne sakamakon taya gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar daya samu a kotun sauraron kararrakin zabe.

KU KARANTA: Tsige Maja Sirdin Sarki ta janyo cece kuce da nuna ma juna yatsa a fadar Sarkin Kano

Sai dai tuni aka yi ta musayar yawu tsakanin Alhaji Idi da kuma manyan hadiman Sarkin Kano, inda Idi ke tabbatar da cewa an tsige shi kuma har an umarceshi ya tashi daga gidan da yake ciki a cikin fadar, yayin da shugaban ma’aikatan fadar, Munir Sunusi ya karyata hakan.

Sai dai Munir yace sun lura ana sace sirdunan dawakan Sarki ne, don haka Shamaki ya kwace makullan dakunan ajiyan kayan adon dawakan Sarki daga wajen Maja sirdi zuwa lokacin da za’a kammala gudanar da bincike.

Amma a yanzu a iya cewa Maja sirdi ya saki dafi, inda ya nemi mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya mayar masa da aikinsa idan har da gaske ba’a tsigeshi daga mukaminsa ba.

Jaridar Punch ta ruwaito Idi ya yi wannan magiya ne a ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, inda yace: “Bani jin haushin kowa a fadar Sarki game da wannan bahallatsa, abin da nake so kawai shi ne Sarki Sunusi ya mayar dani mukamina.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel